Zanga-zanga a Moroko
January 29, 2017Talla
Dubban 'yan kasar Moroko ne suka yi zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suke neman sai a dau matakan yaki da cin hanci, kana a kyautata aikin malaman makarantu. Kimanin kungiyoyin kwadago 1000 suka kira magoya bayansu domin shiga zanga-zangar da aka yi Rabat babban birnin kasar ta Moroko.
Bayaga kungiyoyi kwadago, wasu 'yan jam'iyyun adawa da masu fafitikar kare hakkin jama'a sun shiga zanga-zangar. Daga bisani wasu malaman makaranta kimanin 2000 suka yi dafifi a gaban majalisar dokoki, inda suke cewa dole a soke ayar doka wace ta rage almabashinsu.