1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matan Afghanistan na adawa da dokar sanya kallabi

Ramatu Garba Baba
September 29, 2022

Jami'an Taliban sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa matan da suka fito yin zanga-zangar adawa da dokar sanya kallabi don nuna goyon baya ga matan Iran.

Zanga-zanga kan kisan Mahsa AminiHoto: Markus Schreiber/AP/picture alliance

Jami'an gwamnatin Taliban a Afghanistan, sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa matan da suka fito zanga-zanga, don nuna goyon ga gangamin da ke gudana a makwabciyar kasar Iran kan dokar tilastawa mata sanya kallabi. Daya daga cikin matan da ke wannan fafutukar, ta ce, suna san aika sako na nuna amincewa da gwagwarmayar da 'yan uwansu mata a Iran ke yi na neman 'yanci da walwala.

Kamar yadda al'amarin ya ke a Iran, mata na fuskantar nau'ukan cin zarafi da tsagwama koma a dauresu a duk lokacin da suka fito fili suna neman 'yanci a Afghanistan. Sannu a hankali zanga-zanga kan kallabin a Iran, ta soma yaduwa a sauran kasashen duniya, don ko yau sai da aka kama wasu da suka yi yunkurin kutsa kai a cikin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Oslo na kasar Norway. Boren ya biyo bayan mutuwar Mahsa Amini a lokacin da take tsare a hannun jami'an Hisba kan zarginta da kin sanya hijabi.