1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da manufar kodago ta shugaba Macron

Abdullahi Tanko Bala
September 12, 2017

Dubban jama'a sun gudanar da zanga zanga a Paris domin adawa da manufar shugaba Emmanuel Macron na yin garanbawul ga fannin kodago a kasar

Frankreich Protest gegen die Arbeitsmarktreform in Nizza
Hoto: picture-alliance/dpa/MAXPPP/F. Fernandes

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jawo kakkausar martani bayan da ya kira masu adawa da manufarsa ta garanbawul ga fannin kodago malalata, kalmar da ta tunzura dubban jama'a fitowa kan tituna domin nuna fushinsu.

Yan siyasa da ke adawa da shugaban ciki har da Marine Le Pen sun yi amfani da wannan dama wajen mayar masa da martani da cewa baya kaunar Faransawa.

Macron mai shekaru 39 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Mayu, farin jininsa na kara faduwa kasa wanwar inda masu sharhi ke danganta lamarin da dagawa da kuma kurakurai ta fuskar siyasa.