Jama'ar Sudan na son gwamnatin farar hula zalla
December 19, 2021Da safiyar wannan Lahadi jami'an tsaro suka tsaurara matakan tsaro ta hanyar toshe manyan tituna da gadoji a sassan birnin Khartoum don takawa masu zanga-zangar birki. Sai dai rahotanni na cewa, akasarin gangamin na wannan rana, na tuni ne da cika shekaru uku da soma tattakin da ya kai ga hambarar da tsohuwar gwamnatin tsohon Shugana Omar al-Bashir da kuma dage kan bukatar mika mulki a hannun farar hula.
Gabanin gangamin, a jawabinsa ga 'yan kasa a yammancin ranar Asabar da ta gabata, firaministan kasar Abdallah Hamdok ya yi gargadin cewa juyin-juya halin Sudan yana cikin tsaka mai wuya a sakamakon sabanin ra'ayin siyasa, a lamarin da ya ce, na barazana ga hadin kai da zaman lafiyar kasar.
Tun daga ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata da sojoji suka kwace iko daga hannu Hamdok, kasar ta sake fadawa cikin rudanin siyasa ko da bayan dawo da firaministan mukaminsa da aka yi. Bukatar masu zanga-zangar a yanzu ita ce, mayar da kasar hannu gwamnati mai cikakken mulkin farar hula. Wannan ne karo na tara da al'ummar Sudan ke gudanar da zanga-zangar mai kama da ba-gudu ba ja da baya har sai haka ta cimma ruwa.