1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa na yaduwa a Siriya

March 21, 2011

Bayan boren birnin Deraa na karshen mako, zanga zangar kin jinin gwamnatin Siriya ta yaduwa zuwa kadancin kasar.

Zanga zangar kin jinin gwamnatin Siriya da ta fara tun makon jiyaHoto: AP

A kasar Siriya, zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka fara kwanaki biyun da suka gabata ta yadu zuwa birnin Djasem da ke kudancin kasar. Sai dai sabanin boren birnin Deraa na karshen mako da ya yi awan gaba da rayukan mutane akalla biyar tare da jikata wasu da dama, hukumomi ba su bayar da izinin far wa masu bore ba. Wannan zanga-zangar dai ita ce mafi tsauri da shugaba Bashar El Assad ya fiskanta, tun bayan gadon mahaifinsa akan karagar mulki da ya yi shekaru 11 ke nan da suka gabata.

Daruruwan 'Yan sandan kwantar da tarzoma da ke cikin damara sun shaidar da jana'izar wani matashi da ya rasa ransa, a lokacin tashin hankali da aka fiskanta lahadi tsakanin jami'an tsaro da kuma masu tayar da kayar baya. Ministan shari'a na Siriya yayi tattaki zuwa inda ake gudanar da zanga-zangar domin kwantar da hankulan masu bore ,tare da gayyatansu zuwa kan teburin tattaunawa. Su dai masu zanga-zangar na nuna kosawa da salon mulkin sai mahadi ka ture da kuma katutu da cin hanci da karbar rashawa suka yi a al'amuran gwamnati.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala