1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa ta zama ruwan dare a arewacin Afirka

January 11, 2011

A halin da ake ciki yanzu haka ana fama da mummunar zanga-zanga ta matasa a ƙasashen Tunesiya da Aljeriya, akwai kuma fargabar cewa lamarin zai rutsa da Maroko.

Tashe-tashen hankula da ƙone-ƙonen motoci a sassa daban-daban na ƙasar TunesiyaHoto: picture-alliance/dpa

Tashintashinar sai daɗa yaɗuwa take yi a ƙasar Tunesiya, inda rahotanni suka ce mutane sama da talatin suka yi asarar rayukansu. A can Aljeriya ma an samu rahotannin asarar rayuka sakamakon zanga-zangar matasa. Musabbabin wannan ta da ƙayar baya da matasa suke yi a ƙasashen biyu shi ne matsalar rashin aikin yi da tsadar rayuwa da rashin hangen wata kyakkyawar makoma da rashin adalci da kuma danniya ta 'yan siyasa.

Zanga-zangar adawa da rashin aikin yi da hauhawar farashin kaya a TunesiyaHoto: dapd

Bisa al'ada dai ba a saba ganin hotunan 'yan sanda na amfani da barkonon tsofuwa ko 'yan zanga-zanga na ƙone tayoyin mota akan tituna a ƙasar Tunesiya ba, ƙasar da aka fi saninta a matsayin wani dandalin yawon shaƙatawa. Wani abin mamaki ma shi ne yadda zanga-zangar ta yaɗu zuwa birane da dama na ƙasar. Kuma a halin da ake ciki yanzu haka tuni lamarin ya rutsa da ƙasar Aljeriya, inda matasa suka fara runtuma bisa tituna don huce takaicinsu. Wannan zanga-zangar ta matasa da ƙasashen na yankin Maghreb ke fama da ita tuni tayi sanadiyyar rayukan mutane da dama da kuma wasu ɗaruruwa da suka sami rauni.

Duk wanda yayi kurarin kokawa zai ƙare a gidan yari


Kuma ko da yake ainihin musabbabin tashe-tashen hankulan ya banbanta, amma a haƙiƙa duk tushensu ɗaya ne, wanda shi ne matsalar rashin aikin yi da rashin hangen wani haske game da makomar rayuwar waɗannan matasa dake da shekaru ƙasa da 35 na haifuwa kuma su ne ke da rinjaye a dukkan ƙasashen biyu. Kuma matsalar ba wai ta shafi 'ya'yan talakawa 'yan rabbana ka wadata mu ne kawai ba, abu ne da ya haɗa har da masana da kuma ɗaliban da aka yaye daga jami'a. Rafiƙ mai shekaru 27 daga garin Tala a Tunesiya na ɗaya daga cikin matasan da wannan matsala ta shafa. Ya ce yayi kimanin shekaru uku yana neman aikin yi, amma lamarin ya gagara:

"Tilas sai mutum ya haɗa da toshiyar baki ko wata ƙaƙƙarfar alaƙa kafin ya samu aiki. Idan har ba ka da ikon ba da rashawa kuma ba ka da wata alaƙa ta ƙut-da-ƙut to kai taka ta ƙare. Domin idan har ka yi kurarin kokawa za a tasa ƙeyarka zuwa kurkuku."

In ba aikin yi ba maganar aure


Matasa masu zanga-zanga da ta da ƙayar baya a birnin Annaba dake arewacin AljeriyaHoto: AP

Duk wani matashin da ba ya da aikin yi to kuwa ya shiga uku, saboda ba ya da ikon haya muhallin zama ballatana a yi maganar aure da tanadin wata kyakkyawar makoma. A sakamakon haka duk wani mai iko sai ya tattara nasa ya nasa yayi ƙaura daga yankin na Maghreb. Sai dai kuma a baya ga matsalar rashin aikin yi akwai ta danniyar siyasa, wadda ita ce ma ainihin mafarin rikicin a ƙasar Tunesiya makonni ƙalilan da suka wuce, lokacin da 'yan sanda suka muzanta wa wani matashi dake cinikin kayan miya a birnin Tunis. Wannan taɓargazar da ta faru ita ce ta ta da hankalin matasa suka shiga zanga-zanga a duk faɗin ƙasar. Kazalika a Aljeriya ma, mai arziƙin man fetir, danniyar 'yan siyasa ce ta tasa ƙeyar matasa suka shiga wawason ganima. An saurara daga Werner Ruf, ƙwararren masanin al'amuran Aljeriya yana mai bayanin cewar:

"Cin hanci yayi wa ƙasar Aljeriya katutu. Shuagabannin ƙasar su ne ke wawashe dukiyarta da kuma sayen muggan makamai da ba su yi wa ƙasar amfanin kome."

Wannan dai wani ci gaba ne dake tattare da haɗarin gaske dangane da makomar yankin, inda wasu ƙwararrun masana ke hasashen cewar mai yiwuwa rikicin ya rutsa da ƙasar Maroko nan gaba kaɗan saboda ita ma tana fama da irin wannan matsala dangane da matasanta.

Mawallafi: Ayari/Mudhoon/Lawal

Edita: Abdullahi Tanko Bala