1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar Amirka ta yadu zuwa wasu kasashe

Ahmed Salisu GAT
June 3, 2020

Bayan da kura ta fara lufawa a zanga-zangar adawa da kisan bakar fata a Amirka, zanga-zangar ta yadu a halin yanzu zuwa wasu kasashen duniya musamman na Turai.

USA Washington Lincoln Memorial | nach Tod George Floyd durch Polizeigewalt in Minneapolis | National Guard
Hoto: Getty Images/W. McNamee

Rahotanni daga Amirka na cewar an soma samun saukin na zanga-zangar da 'yan kasar ke yi a wasu jihohin kasar don nuna rashin amincewa da kisan da 'yan sanda suka yi wa bakar fatar nan George Floyd a kwanakin da suka gabata. To sai dai duk da wannan, a wasu sassan duniya ciki kuwa har da nan nahiyar Turai da kuma Afirka al'umma na ci gaba da gudanar da zanga-zanga don nuna rashn amincewarsu da kisan na Mr. Floyd.

Jami'an tsaron a wasu daga cikin jihohin Amirka sun shaida cewar an samu raguwar mutanen da ke fantsama kan tituna domin nuna hushinsu kan kisa George Floyd da wani dan sanda ya yi, sannan sun ce an samu raguwar fasa shaguwa da sauran dukiyoyi na al'umma musamman ma a New York, kuma wannan sauki da aka samu na da nasaba da dokar hana fita da aka sanya, wadda za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar bakwai ga wannan wata da muke ciki.

To sai dai duk da saukin da aka samu a Amirka din, a wasu sassan duniya kuwa jama'a na ci gaba da fantsama kan tituna don gudanar da zanga-zanga. A birnin Rotterdam na kasar Holland ga misali dubban mutane ne suka hadu domin yin zanga-zangar a kan fitacciyar gadar nan ta Erasmus Bridge da ke da ke birnin:

Zanga-zangar adawa da kisan Geroge Floyd a birnin LandanHoto: Reuters/H. McKay


Wannan cikowa da aka yi ce ma ta sanya 'yan sanda shawarta masu zanga-zangar kan su hakura su koma gida domin kuwa jama'a sun gaza kiyaye ka'idar nan ta ba da tazara da aka sanya domin dakile yaduwar cutar nan ta Coronavirus. Can ma a birnin Landan na Birtaniya haka lamarin yake inda jama'a da dama suka hadu don yin zanga-zanga kan kisan na George Floyd. Sai dai irin tsarin da suka yi amfani da shi ya sha banban da irin wanda aka gani a Holland domin masu zanga-zangar na sanya ne da takunkumi kuma sun mutunta dokar nan ta ba da tazara. Karen Koroma guda ce daga cikin masu wannan zanga-zanga:


"George Floyd ba wai bakar fata ba ne kadai, zai iya kasancewa abokinka ko dan uwa ko ma mahaifi. Manta da batun banbancin launin fatarsa, ya kamata mu fahimci cewar abin da ya faru gareshi zai iya faruwa gareni ko kuma a gareku. Ina fatan jama'a za su fahimci hakan kuma ina fatan hakan zai hade kanmu baki daya a matsayin al'umma daya".

Yayin da jama'a ke ci gaba da nuna rashin amincewarsu da irin abubuwan da ke wakana a Amirka musamman ma zargin da ake yi wa 'yan sanda da wasu mutane na aikata ba daidai kan bakaken fata a kasar, hukumomi na ci gaba da daukar matakai na ganin an kawo karshen ta da kayar bayan da ake ci gaba da yi. Irin matakan da ake dauka kuma tuni suka fara haifar da kace-nace tsakanin shugaban kasar ta Amirka Donald Trump da wasu mukarraban gwamnatinsa. Na baya bayanan shi ne irin matsayin da sakatar harokin tsaron kasar Mark Esper ya dauka na kin amincewa da dokar da shugaban kasar ke son amfani da ita ta girke sojoji cikin damara a kan tituna don kawo karshen zanga-zangar:

Hoto: Reuters/L. Wasson


"Kamata ya yi a ce an yi amfani da sojoji don tabbatar da doka da oda a matsayin mataki na karshe sannan ya kyautu ne a ce an yi hakan a lokutan da lamura suka kai magaryar tukewa. A iya sanina ba mu kai wannan matsayin ba a yanzu don haka ba na goyon bayan amfani da dokar da za ta bai wa shugaban kasa damar baza sojoji cikin shirin yaki a kan titunanmu".

Yanzu haka al'ummar Amirka da ma wadanda ke sanya idanu kan lamuran da ke kai-komo dangane da wannan zanga-zanga na zuba idanu don ganin yadda za a kwashe kan wannan batu tsakanin shugaban kasar da sakataren tsaronsa da kuma irin matakan da za a ci gaba da dauka wajen ganin lamura sun daidaita a kasar.