Zanga-zangar dalibai likitoci a Aljeriya
January 9, 2018Hotuna da ake yadawa ta kafoyin sadarwa na zamani a kasar ta Aljeriya sun yi ta nuni da yadda daruruwan likitocin suka hallara a harabar asibitin koyarwa ta birnin Oran da ke da nisan km 400 a yammacin Alger babban birnin kasar ta Aljeriya, inda daga bisani masu jerin gwanon suka soma tattaki ya zuwa ofishin shugaban gunduma.
Kusan dalibai likitoci 5000 ne suka hallara domin nuna adawarsu ga matakin. A ranar uku ga wannan wata na Janairu ma dai jami'an tsaro sun tarwatsa wani yunkurin jerin gwano na likitocin, inda suka ce bai samu izini ba. A cikin dokar kasar ta Aljeriya dai, duk wanda ya kammala karatunsa na aikin kwararren likita, to ala tilas sai ya yi shekara daga daya har zuwa hudu yana aiki a daya daga cikin garuruwa masu nisan gaske na kasar.