1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar Iran: Trump na tunanin daukar matakin soji

January 12, 2026

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana nazarin matakai masu tsauri kan zanga-zangar Iran, ciki har da yiwuwar amfani da karfin soja, yayin da Tarayyar Turai ke shirin kakaba takunkumai.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Alex Wong/Getty Images

Da yake magana da manema labarai a cikin jirgin Air Force One, Trump ya ce Iran ta kusa ta ketare abin da ya kira layin gargadinsa, yana mai cewa rundunar sojin Amurka na nazarin matakai masu karfi.

Shugaban na Amurka ya kuma ce zai tattauna da attajirin duniya Elon Musk kan yiwuwar amfani da tsarin intanet na tauraron dan Adam, Starlink, mallakinsa domin bai wa ‘yan Iran damar shiga intanet.

Sai dai Shugaba Trump ya ce Iran tuni ta fara nuna sha'awar tattaunawa da shi. Amma  ya yi gargadin cewa Amurka na iya daukar mataki kafin ganawar saboda ci gaba da zanga-zanga da kuma cin zarafin masu zanga-zangar.

Karin bayani: Iran ta sha alwashin daukar fansa muddin Amurka ta kai mata hari

A gefe guda, babbar jami'ar diflomasiyyarTarayyar TuraiKaja Kallas ta ce za ta gabatar da shawarwarin kakaba sabbin takunkumai kan Iran, bisa abin da ta kira murkushe masu zanga-zangar da karfi.