Najeriya: Zanga-zangar jam'iyyar ADC a Abuja
April 8, 2026
Zanzan-zanga ce ta lumana da yayyan jam'iyyar ADC da suka wo takaka daga sassan Najeriya suka hallara a Abuja hedikwatar kasar, inda suka yi tattaki a wasu manyan tituna suna rera take da wakoki na shagube da habaici a kan matakin da hukuar zaben Najeriyar ta dauka a kan jam'iyyarsu ta ADC, abin da ya jefa jam'iyyar a cikin halin tsaka mai wuya.
Dalilin zanga-zangar
Fitowar jiga-jigan jamiyyar ta ADC da suka hada da sakatarenta na Najeriya Rauf Argebesola da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da dan takarar neman shugaban kasa a jam'iyyar Labour a 2023 Peter Obi ya karawa zanga-zangar armashi bisa ga matsin lambar da suke yi. Aisha Yesufu yar jamiyyar ADC ce da ke kusa da Peter Obi ta shaida man abin da suke bukatar ganin an yi, wanda yake dangantawa da neman dagula matsayin 'yan adawa.
Masu zanga-zanga da sauran sassan kasar
Fargabar maida Najeriyar kasa mai jamiyya daya ya sake tasowa a wajen zanga-zangar da yan jamiyyar ADC suka yi a Abuja abinda Tasiu Adamu Al-Amin daga Kano ya bayyana cewa kofa wayo ya san na ki.
Kwamishinan hukuamr zaben Nakeriya Farfesa Abdullahi Zuru shi ne ya karbi rubutaccen sako dauke da bukatun masu zanga-zangar. A yanzu 'yan jam'iyyar ta ADC sun ce za su ci gaba da matsin lamba tare da duba damar da suke da ita ta shiga zaben Najeriya da za a yi a shekara ta 2027.