Mutane sun fusa da dauke wutar lantarki
January 25, 2023Dubban sun yi zanga-zanga kan titunan kasar Afirkia ta Kudu a wannan Laraba domin nuna takaici kan matsalolin makamashi na hasken wutar lantarki da ake samu lamarin da ke tabarbara lamura a kasra mafi ingancin tattalin arziki na zamani a nahiyar Afirka. Masu zanga-zangar sun yi dafifi a gine-ginen gwamnati a birnin Johannesburg da sauran biranen kasar.
Galibin masu zanga-zangar sun yi shiga kamar na jam'iyyar adawa ta DA wadda ta bukaci a gudanar da gangamin adawa da gwamnatin kasar karkashin jam'iyyar ANC.
Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ta Afirka ta Kudu a wannan makon ya bayyana cewa ya fahimci irin rashin jin dadi da mutane suke nuna bisa yanayin da kasra ta samu kanta, amma ya ce ba matsaloli da za a magance rana daya ba, domin haka ana bukatar hakuri.