1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Gangamin adawa da matakan yaki da corona

Abdoulaye Mamane Amadou
August 1, 2021

Duk da hukuncin kotu na hana yin gangami masu adawa da matakan yaki da cutar corona a Jamus sun gudanar da zanga-zanga a birnin Berlin, a ci gaba da fafutikarsu ta neman 'yanci.

Demonstrationsverbot in Berlin I Querdenker
Hoto: Fabian Sommer/dpa/picture alliance

Dubban mutane masu adawa da matakan yaki da corona a tarayyar Jamus, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Berlin, duk da matakan da hukumomin kasar suka dauka na haramta zanga-zangar.

Masu aiko da rahotanni sun ce an yi dauki ba dadi tsakanin 'yan sandan kwantar da tarzoma da masu boren, a yayin da suka kudri anniyar karya shingen 'yansanda a unguwar "Charlottenburg" da ke yammacin birnin Berlin, kafin yan sandan sun yi amfani da tiyagaz da kulake don tarwatsa masu zanga-zangar, tare da kama wasu da dama.

Fiye da 'yan sandan kwantar da tarzoma 2000 ne hukumomin Jamus din suka girke a birnin Berlin da zummar murkushe masu zanga-zangar kin jinin matakan yakin da corona da kasar take dauka, suna masu cewa matakan na daga cikin na kan gaba wajen hana 'yan ci da walwalar jama'a.