1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus: Zanga zangar matasa a Yuganda

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 27, 2024

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhinta mai taken: An cafke matasan "Generation Z" da ke zanga-zangar yaki da cin-hanci a Yuganda bayan sun tunkari majalisar dokoki,

Zanga zangar matasa a Kenya
Zanga zangar matasa a KenyaHoto: James Wakibia/SOPA Images/ZUMA Press Wire/picture alliance

Matasan na neman a kawo karshen cin-hanci da rashawa da kuma kawo gyara a hanyar tafiyar da gwamnati. Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce jami'an tsaron kasar da ke yankin gabashin Afirka, sun yi abin da suka saba wato murkushe masu zanga-zangar da karfin tuwo. Kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito, jami'an tsaron sun cafke masu zanga-zangar da suka tunkari majalisar dokoki sama da 50. Masu gabatar da kara sun shaida wa kotu cewa, matasan na zanga-zanga ne a tsakiyar hanya.

Wasu daga cikin Jaridun JamusHoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Kenya ta samu sabuwar gwamnati bayan matasan Gen Z sun yi ta zanga-zangar adawa da sabuwar dokar haraji in ji mujallar FAZ.NET. Ta ce bayan kwashe tsawon makonni suna zanga-zanga, Shugaba William Ruto na Kenya ya yi alkawarin daukar matakan gyara yayin wata tattaunawa da ya yi a gidan talabijin. A Larabar da ta gabata, Shugaba Ruto ya ayyana mambobin sabuwar majalisar zartaswarsa wanda za a jira majalisar dokoki ta amince da su. FAZ.NET ta ce daga cikin sunayen da Ruto ya mika ga majalisar dokokin, har da mambobin babbar jam'iyyar adawa ta tsohon firaministan kasar  Raila Odinga wato Orange Democratic Movement ODM.

Ta ce zanga-zangar ta tsawon makonni kan adawa da sabuwar dokar haraji a kasar ta Kenya da ta yi sanadiyyar asarar rayuka 54, ta tilasta Ruto janye kudirin dokar tare da hawa teburin tattaunawa. Shugaba Ruto ya kuma mika sunan Douglas Kanja da ke rike da shugabancin Sifeto Janar na 'yan sanda bayan tsohon Sifeto Janar na 'yan sandan Japhet Koome ya ajiye aiki saboda sukar yadda ya tunkari masu zanga-zangar, a matsayin sabon Sufeto Janar na 'yan sandan Kenyan.

Birnin Khartoum mai fama da rikiciHoto: Ahmed Satti/AA/picture alliance

Za mu karkare da jaridar Neue Zürcher Zeitung a nata sharhin mai taken: Da tallafin Switzerland za a samu tsagaita wuta a Sudan, bayan da Amurka ta bukaci a shirya sabuwar tattaunawa tsakanin bangarorin da ke yakar juna. Jaridar ta ce a shekarar da ta gabata ce Switzerland ta fara daukar matakin shiga tsakanin domin sulhunta rikice-rikice, a yanzu bayan tattaunawa kan yakin Rasha da Ukraine wata tattaunawar za ta biyo baya. A watan Agustan da ke tafe, Switzerland din za ta karbi bakuncin tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin da ke yakar juna a Sudan kamar yadda sakataren harkokin kasashen ketare na Amurka Antony Blinken ya bayyana a Talatar da ta gabata.

Tsawon sama da shekara guda ke nan, yakin basasa ya barke a Sudan tsakanin sojojin gwamnati karkashin shugaban kasar Abdel Fattah al-Burhan da dakarun Rapid Support Forces (RSF) karkashin jagorancin Janara Mohammed Hamdan Daglo. Rikicin da kawo yanzu ya tarwatsa sama da mutane miliyan 10, tare da halaka kimanin dubu 150. A ranar 14 ga watan Agustan da ke tafe ne dai, ake sa ran za a fara tattaunawar karkashin jagorancin Amurka da nufin cimma wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta. Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin bayar da agaji ya nunar da cewa sama da mutane miliyan 25 kimanin rabin al'ummar kasar ke nan, ba su da abin da za su ci yayin da tuni wasu sama da dubu 755 ke fama da matsananciyar yunwa.