1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sojoji sun mamayi masu zanga-zanga

October 19, 2020

A yayin da ake ci gaba da zanga-zangar da matasa ke yi a Abuja da ma ragowar biranen Tarayyar Najeriya da dama, gwamnati ta fito da sojoji kan tituna a birnin na Abuja, abin da ke nuna alamun karshen hakurin mahukuntan.

Nigeria Abuja | End Sars Proteste | Demonstranten
Masu zanga-zanga sun yi kokarin rufe hanyoyin shiga da fita birnin AbujaHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Duk da cewar dai ta share kwanaki da daman gaske tana lalama da ban hakuri, daga dukkan alamu ana shirin kai karshen hakurin mahukuntan Tarayyar Najeriyar, wadanda a wannan Litinin din suka baza sojoji a titunan Abuja fadar gwamnatin kasar da nufin kai karshen jerin zanga-zanga da matasan ke yi. Matasan dai ba su boye aniyarsu ta tsayar da daukacin harkokin birnin ba, bayan da suka rika aike sakon toshe kafofi na shiga birnin tun daga karshen mako. Kuma tun da sanyi na safiyar Litinin din wannan makon ne dai, suka rika tururuwar cika alkawarin nasu bayan da suka toshe muhimman tituna guda uku da ke hade Abujar da ragowar sassan kasar dabam-dabam.

Karin Bayani: Najeriya: Ana zubar da jini a Arewa

Sai da ta kai ga jibge jami'ain soja da 'yan sanda a kofofin shiga gari, kafin iya kai wa ga kyale ma'aikata da ma ragowar jama'ar gari isa ga Abujar domin harkokinsu.
To sai dai kuma ko bayan kokarin hana kai wa ga shiga garin dai, matasan kuma a karon farko sun nemi isa  har ya zuwa fadar shugaban kasar, kafin haduwa da fushi na jami'an tsaron da suka rika harba musu barkonon tsohuwa domin tarwatsa su. Esther Jonathan dai na zaman daya cikin masu zanga-zangar da kuma ta ce suna zaman jiran fara aiwatar da jerin alkawarin nasu, kafin saukowa daga dokin zanga-zangar da suka share kwanaki 11 suna tafkawa. Kokarin cika alkawari na matasan, ko kuma tayar da hankalin al'umma a gari dai, daga dukkan alamu sauyi na salo na masu zanga-zangar ya bata ran mahukuntan kasar, a fadar Sunday Dare da ke zaman minista na matasan Tarayyar Najeriyar, da kuma ya ce matasan na bukatar takawa a hankali.

'Yan sanda na cin zarafin masu zanga-zanga a NajeriyaHoto: Reuters/Str

Karin Bayani: Murna bayan rusa rundunar SARS a Najeriya

Daya bayan daya dai manyan jagororin zanga-zangar na janyewa, sakamakon sabon matakin da wasunsu ke ganin ya wuce da bukatar farko ta sauya tsarin 'yan sanda a kasar. Rundunar 'yan sandan dai ta fara shirin cika alkawarin da ta dauka,  na horar da sabuwar rundunar SWAT  da za ta maye gurbin SARS din da ta kunshi 'yan sanda 1850 a yanzu..

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani