Shin yin addu'o'i ne mafita ga Najeriya?
August 7, 2024Bayan kwashe kwanaki ana zanga-zangar a sassa da dama na Najeriyar ne, al'ummomin jihohin Arewa maso Gabashin kasar suka sauya salo ta hanyar rungumar yin azumi da addu'o'in neman mafita kan halin kunci da yunwa da ake ciki. Da yawa sun karbi wannan shawara saboda a cewarsu ita ce hanyar da ta fi dacewa, maimakon hawa kan hanya a zanga-zangar da ke kai ga barnata kayan al'umma da kuma yin fito na fito da hukumomi baya ga jami'an tsaro da ke janyo asarar rayuka ko jikkata mutane wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba.
Matasa kan hadu a wurare su yi sallolin nafila da karatun al-Qur'ani mai girma da yin addu'o'i da suke ganin shi ne zabin da ya saura mu su, inda tuni wasu ke karfafa amusu gwiwa da kuma samar musu da abinci. Suma shugabannin 'yan kasuwa sun fara yin addu'o'in da yin sadaka tare da kira ga mambobinsu a duk inda suke su rungumi yin addu'ar, domin samun mafita. Sai dai bayan saukin da aka samu na zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriyar da ya bayar da damar komawa harkokin yau da kullum, kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun nemi a gudanar da bincike na mutane da aka halaka tare da bi mu su hakkinsu na shari'a.