An yi bore a harabar majalisar Ukraine
June 19, 2018Talla
Masu boren sun hada da tsoffin masu hakar ma'adinai da wadanda suka taimaka wa kasar a yakin Afghanistan a zamanin rusashen Hadeddiyar Daular Soviet a shekaru 33 da suka gabata, inda suke neman gwamnati ta kyautata rayuwarsu da karin alawus.
A yanzu dai an jibge karin 'yan sanda 500 a harabar majalisar, yayin da mataimakin kakakin majalisar Iryna Gerashchenko ya bukaci ganawa da wakilan dukkannin bangarorin da ke boren.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun hatsaniya tsakanin 'yan sanda da tsofoffin mazan jiya a harabar majalisar Ukraine ba, inda ko a watan Maris sai da rikicin ya barke sannan wani rikin ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu a shekarar 2015.