'Yan Shi'a sun yi zanga-zanga a Najeriya
June 26, 2020Talla
Magoya bayan kungiyar Islamic Movement of Nigeria IMN sun gudanar da wata zanga-zangar bukatar gwamnatin Najeriya hanzarta sakin jagoran kungiya Sheick Ibrahim Yakub El- Zak zaky da mai dakinsa, wadanda ke daure a gidan kurkukun jihar Kaduna yau tsawon watanni.
Da yake magana da manema labarai kan dalilansu na fitowa zanga-zanagar, Kakakin kungiyar IMN Sheik Aliyu Umar Turmizy ya shedawa wakilinmu dalilansu na fitowa yin tattaklin a yau yana mai cewa suna bukatar ne ganin gwamnatin jihar Kaduna ta sako jagoransu ne biyo bayan wata kotu a Najeriya ta umarci yin haka tun daga farko.
Masu zanga-zangar dai sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta daukar matakan kare kashe-kashin al'umma a yankin Arewacin Najeriya.