Zanga-zangar neman sauyi a Yemen
April 4, 2011Wata jaridar Amurka ta ce gwmantain ƙasar ta fara yin wani yaunƙuri na neman shugaba Ali Abdallah Saleh na Yemen da ya sauka daga kujerar mulkin ƙasar. Majiyoyi daga gwamnatocin Amurka da na Yemen sun faɗawa kamfanin dillancin labarun Jamus cewa a yanzu haka gwamnatin Shugaba Barack Obama ta yi ammanar cewa Saleh ba zai iya gudanar da sauye-sauyen da suka dace ba a ƙasar.
Amurka dai bata yi wa shugaban na Yemen wannan sukar a fili ba, duk da cewa ana kallon shugaban a matsayin wanda ke ƙawance da Amurkan wajen yaƙi da ta'addanci.
A ƙarshen wannan makon da ya gabata ne jamiyyun adawan Yemen suka fitar da wani shiri inda suka buƙaci shugaba Saleh da ya sauka ya kuma miƙa ragamar mulki ga mataimakin sa, shirin da shugaban ya yi watsi da shi ya kuma ce ba za a sauke shi daga kujerar mulki ba da on ran sa ba.
Jami'an tsaro dai sun cigaba da tursasa wa waɗanda ke zanga-zangar neman shugaban ya sauka, kuma kawo yanzu mutane 52 suka hallaka tun bayan da aka ƙaddamar da zanga-zangar neman sauyi a ƙasar a watan fabrairun da ya gabata.
Mawallafiya:Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal