Zanga-zangar nuna adawa da taron G20 a Hamburg
July 2, 2017![Protestwelle gegen den G20 Gipfel](https://static.dw.com/image/39511991_800.webp)
Talla
'Yan sanda sun ce kamar mutane dubu goma ne suka yi zanga-zangar cikin ruwan sanhi a gaban ofishin magajin gari na birnin na Hamburg inda za a yi taron. Daya daga cikin masu gangamin ya soki lamirin kasashen na G20 da cewar su, suka fi kowa fitar da hayakin da ke gurbata muhali a duniya amma kuma ba sa yin wani yunkuri don rage hayakin.