Gangamin nuna goyon bayan soji a Biurkina Faso
May 1, 2025
Dubun dubatar jama'a sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatin mulkin soja a Burkina Faso, kwanaki bayan da ta ce ta dakile wani yunkurin juyin mulki.
Burkina Faso ta ce ta dakile yunkurin juyin mulki
Dauke da alluna masu nuna alamun goyon baya ga gawamnatin ta rikon kwara, da kuma shugaban kasar Ibrahim Traore, masu zumudin mulkin na soji sun furta kalamai masu kara jaddada goyon bayansu da yanayi na tafiyar harkokin mulkin soji a Ouagadougou babban birni da nuna adawarsu da duk wani katsalandan na manyan kasashe, da salon mulki irin na yammacin duniya.
Mayakan jihadi sun kashe sojojin Benin 70
Wannan ce zanga-zangar goyon bayan gwamnatin mulkin soja mafi girma da aka yi a kasar, tun bayan wata makamanciyarta da aka gudanar jim kadan bayan da sojoji karkashin jagorancin Ibrahim Traore suka karbe mulki.