Zanga zangar Pakistan ta zama rikici
January 15, 2013Talla
'Yan sandan kasar Pakistan sun yi amfani da hayaki mai saka hawaye, kan masu zanga zanga, kuma anji karar bindigogi, yayin da masu zanga zangar da ke kifan 'yan sandan da duwatsu, su ka yi yunkurin isa majalisar dokoki a wannan Talata.
Wani malamin dan kasar mai takardun zaman Canada, Tahir-ul Qadri ya shirya gagarumar zanga zangar ta kwanaki biyu zuwa Islamabad babban birnin kasar, domin neman gudanar da sauye sauye da su ka hada da kafa gwamnatin rikon kwarya, domin gudanar da zabe mai zuwa, tare da kuma ganin an kawar da matsalar cin hanci da rashawa.
Kamafanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya ce babu tabbacin wanda ya fara janyo hargitsin.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu