1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zanga-Zangar Senegal na ci gaba da janyo asarar rayuka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 11, 2024

Majalisar dokokin kasar ta amince da dage zaben Fabarairun nan har sai zuwa Disamba. Kuma duk da cewa wa'adinsa na biyu zai kare ne a watan Afrilu mai zuwa, to amma zai ci gaba da shugabancin kasar har sai an yi zabe

Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Mutum na uku ya mutu a yankin Ziguinchor na Senegal mahaifar jagoran adawa Ousmane Sonko, bayan arangama da 'yan sanda lokacin zanga-zangar kin amincewa da matakin shugaba Macky Sall na dage zaben shugaban kasa.

Karin bayani:Siyasar Senegal da mutuwar shugaban Namibiya a jaridun Jamus

Wani 'dan jam'iyyar adawa ta PASTEP mai suna Abdou Sane, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa matashin mai shekaru 19 ya rasu ne bayan harbinsa a ka, kuma wasu da dama sun jikkata, bayan da aka shiga rana ta uku ta zanga-zangar.

Karin bayani:Majalisa ta amince da dage zabe a Senegal

Majalisar dokokin kasar ta amince da bukatar shugaba Sall wajen dage zaben daga 25 ga wannan wata na Fabarairu da muke ciki, har zuwa watan Disamba. Kuma duk da cewa wa'adin zangon mulkinsa na biyu zai kare ne a watan Afrilu mai zuwa, to amma majalisar dokokin ta amince ma sa da ya ci gaba da rike matsayin shugaban kasar har sai an zabi wani sabo.