Sojojin Najeriya sun yi bore a Maiduguri
August 13, 2018Sojojin wadanda suka fusata sun ki shiga jiragen sama da aka shirya kwashe su zuwa sabon wurin aikin su da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno, inda su ka yi ta yin harbi a sama. Sojojin sun kuma yi barazana ga man'yan jami'an su da suka nemi rarrashin su domin zuwa sabon wajen aiki.
A cewar Sojojin, sama da shekaru hudu suna yaki da Boko Haram a Borno ba tare da an maida su wuraren su na asali ba, abinda su ka ce ya saba da yanayin aikin Sojoji. Daya daga cikin Sojojin da ya bukacin DW ta sakaya sunansa, ya bayyana cewa: "Mun hau Bom, an harbe mu an mana kwanton bauna, duk muna nan tsawon shekaru hudun nan. Bama samun lokacin iyalanmu tsanani a baka kwana 14 ka je ka ga iyalanka, Saboda haka mun yi kokarinmu a kawo wasu. Shi ya sa muke zanga-zanga saboda Janar Buratai ko Shugaba Buhari su ji halin da muke ciki”
Sani Umar wani mai sharhi kan harkokin tsaro, ya ce: "Yanayin na da hadari, ya kamata mahukunta su gaggauta daukar mataki."
Lamarin ya jefa jama'ar gari cikin fargaba, amma rundunar Sojin Najeriyar ta ce kura ta lafa kuma wasu tsirarun Sojoji ne ke neman turje wa sauyin wurin aiki, wanda kuma ba bakon abu bane. Boren Sojojin na zuwa ne bayan da wasu ‘yan sanda suka yi bore a Maiduguri saboda rashin biyan su hakkokinsu.