Zanga-zangar Sudan na kara tsanani
December 24, 2018Talla
A wannan Litinin ce a cewar likitocin na Sudan za su fara yajin aikin, koda yake sun ce suna iya duba masu bukata ta gaggawa.
Kungiyar ta kuma ce lallai ne su nuna fushin saboda karfin da jami'an tsaro suka yi amfani da shi kan jama'a.
An dai yi zargin jami'an tsaron na Sudan sun yi amfani da harsasan gaske kan masu zanga-zangar, inda akalla mutum tara ne aka tabbatar da mutuwarsu.
Zanga-zangar ta faro ne a makon jiya a wasu biranen gabashin Sudan din, tuni kuwa ta bazu zuwa wasu sassanta.