Zanga zangar neman kifar da gwamnati
December 24, 2018Masu zanga zanga a fadar mulkin kasar ta Sudan sun dai kai ga rera taken nuna kyamar gwamnatin Shugaba al- Bashir, wanda ya yi shekaru 30 ba daya yana mulkin kasar ta Sudan.
Wata mata daga cikin masu zanga zangar ta ce su ba masu neman tashin hankali ba ne, kamar yadda wasu jami’an gwamnati ke zargi. Kokari suke yin a kare mutuncinsu wand aba zai yiwuwa ba sai da abinci da ilimi da lafiya.
Zanga zangar dai ta bazu a garuruwa, a jihar Nilul Abyadh da ke gabashin kasar ta Sudan, a kudu da birnin Khartum, rahotanni na nuni da cewa, masu Zanga-zangar sun kone gidan gwamna da wasu gine-ginen gwamnati.
Ministan watsa labarai na kasar dai, Busharah Juma’a Aro ya zargi Jami’an leken asirin Isra’ila Mosad da kitsa zanga zangar neman rusa Sudan. Jami’an kwantar da tarzoma dai, sun yi ta harba barkonan tsohuwa da harsashin roba don tarwatsa masu zanga zangar.
Tun ranar Larabar da ta gabata ne dai mutanen Sudan suka fara gudanar da zanga zangar nuna kin amincewa da karin kudin buredi da kuma tsadar rayuwa.
A shekarar da ta gabata, farashin wasu kayayyaki ya nunka, kuma hauhawar farashi ya kai kusan kashi 70 cikin 100, kuma darajar kudin Sudan wato Jinai ta fadi warwas, kuma an rika samun karancin kayayyaki a manyan biranen kasar har da Khartoum.