Zanga-zangar 'yan adawa a Kenya
September 13, 2026
Dubban mutane sun yi zanga-zanga a birnin Nairobi na kasar Kenya a wannan Lahadi, duk da tsoron da ake ji na yuwuwar samun tashin hankali. Dan siyasa na bangaren adawa Edwin Sifuna mai shekaru 44 da haihuwa ya kira wannan zanga-zangar domin nuna takaicin yadda cin hanci da rashawa gami da tashe-tashen hankula na siyasa suka zama ruwan dare a kasar.
Shirin zaben Kenya
Shi dai Sifuna ana gani ya kara zama babban wanda zai kalubalanci Shugaba William Ruto a zaben kasar na shekara mai zuwa ta 2027.
Ita kanta hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa, Human Rights Watch (HRW) ta ce cikin wannan makon mutane shida suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikata sakamakon tashe-tashen hankula a wajen tarukan siyasa a kasar ta Kenya da ke yankin gabashin nahiyar Afirka.