Najeriya: Zargin 'yan sanda da cin-zarafi
November 28, 2024Bincike ne mai zurfi kungiyar ta ta yi a kan abin da ya faru, a lokacin da matasan Najeriyar suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa ta tsawon kwanaki 10 a watan Augustan da ya gabata. Amnesty ta ce ta tattara bayanai daga shaidu na gani da ido da ma abin da jami'anta suka shaidar a kan yadda 'yan sandan Najeriyar suka yi amfani da karfin da ya wuce iyaka a kan masu zanga zangar a jihohi shida na kasar da Abuja. Matasan dai sun ta artabu da 'yan sanda a kan zanga-zangar da suka yi ta nuna koken cewa rayuwa ta yi masu tsada, musamman a jihohin da suka hadar da Kaduna da Kano da Jigawa da Borno da ma babban birnin tarayya Abuja.
Matasan da suka shiga zanga-zangar sun yi ta koken abubuwan da suka faru, Kwamared Yahya Abdullahi na cikin matasan da suka shiga zanga-zangar a wancan lokaci, ya mayar da martani a kan rahoton na kungiyar Amnesty International din. Duk da shidun da kungiyar ta Amnesty International ta bayyana da ta bankado a rahoton nata da ya shaidar da kame mutane 1,200 ciki har da mata da yara kanana, rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi ta musanta cewa ta yi amfani da karfi a kan masu zanga-zangar tare da cewa jami'anta ma aka jikkata. Binciken na Amnesty International ya sake tono abubuwa da dama da kungiyoyin farar hula ke rajin lallai sai gwamnati ta dauki mataki a kai, inda bayan sakin wasu daga cikin wadanda aka kama akwai batun biyan diyya ga 'yan uwansu da gwamnati ta yi shiru a kai.