1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta yi zargin cin zarafin kananan yara a Najeriya

Uwais Abubakar Idris GAT
May 27, 2020

Wani rahoton bincike da kungiyar Amnesty International ta fitar a wannan mako ya yi zargin cin zarafin kananan yara da sojojin Najeriya da kuma kungiyar Boko Haram ke yi a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Flüchtlingslager Minawao in Kamerun
Hoto: DW/M.-E. Kindzeka


Kungiyar kare hakin dan Adam ta kasa da kasa ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto wanda ya gano mumunan halin da yara kanana ke ciki a yankin Arewa maso gabashin Najeriya saboda garkuwa da su da ake yi da tursasa masu aikin soja da kungiyar Boko Haram ke yi a yankin. Rahoton mai shafuka 91 wanda yake ta da hankali sosai inda kungiyar ta Amnesty International ta bankado zargin da take na yadda sojojin Najeriyar suka rinka azabtarwa da kule yara kanana barkatai, abin da ya kara ta'azara hali na cin zarafi da aikata liafufuka yaki da yaran suka shiga a hannun 'ya'yan kungiyar Jama'atu Ahlu Sunnah Li Dawwati Waljihad a jihohin Borno da Adamawa.

Rahoton da kungiyar ta Amnesty ta yi wa take da ''Hawayenmu sun kafe '' ya bayyana yadda daukar tsawon shekaru 10 ana gwabza yaki tsakanin sojojin Najeriya da kungiyar ta Boko Haram ya kasance cin zarafi ga yara kanana a yankin arewa maso gabashin Najeriyar da ya sanya Najeriyar fuskantar hatsarin asarar daukacin jinsi alumma in har ba'a dauki wani mataki ba.

Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Jimlar mutane 230 ne Kungiyar Amnesty International ta yi hira da su a tsakanin watan Nuwamba na 2019 zuwa Afrilu na 2020 wadanda suka hada da yara 119 wadanda yara kanana ne a lokacin da aka gana masu azaba ta laifufukan yaki a kan lokacin da suke a hannun kungiyar ta Boko Haram. Malam Kabiru Adama masani a kan harkokin tsaro ya bayyana hatsarin wannan hali a yankin na arewa maso gabashin Najeriya.

Hoto: Thomson Reuters Foundation/O. Okakpu


Kungiyar ta Amnesty International dai ta ja hankalin Kungiyar Tarayyar Turai da ma sauran masu ba da tallafi cewa suna daukan nauyin sukurkutaccen shiri na talafa wa mutanen da suka shiga matsala a hannun 'yan Boko Haram a Najeriya wanda sojoji ke aiwatarwa da ta yi wa lakabi da ''tudun na tsira''. Za sa ido don jin martanin da sojoji za su fitar a kan wannan rahoto da a baya takan yi watsi da shi.