1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniFaransa

Faransa: Zargin dan wasan linkaya da fyade

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 15, 2026

An tuhumi dan wasan linkaya na Faransa, Yannick Agnel wanda ya samu lambar zinare a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya wato Olympic, sakamakon zarginsa da aikata laifin fyade.

Faransa | Zargi | Fyade | Yannick Agnel | Wasan Linkaya
Zargin dan wasan linkayar Faransa da aikata fyadeHoto: Nicolas Rongier/Hans Lucas/AFP/Getty Images

Sai dai dan wasan Linkayar Yannick Agnel, na ci gaba da yin watsi da wannan zargi na fyade. Tun cikin watan Mayu lauyoyi suka daukaka kara kan zargin fyaden da ake yi wa dan linkayar mai shekaru 33 a duniya. A tsawon wasannin linkayar da Agnel ya yi, ya samu lambobin zinare biyu kana yana cikin wadanda suka yi fice a wasannin linkaya a Faransa.