1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zargin gwamnatin Najeriya da biyan kudin fansa

September 1, 2025

A yayin da mahukuntan Najeriya suke bugun kirjin kan yaki da ta'addanci a yankin arewa maso yammacin kasar, tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufa'I dai ya zargi mahukuntan Abuja da biyan kudin fansa ga barayin daji.

Jami'an tsaron Najeriya
Jami'an tsaron NajeriyaHoto: Audu Marte/AFP/Getty Images

 

Dubban miliyoyin Nairori ne dai ake fadin masu ta'adda sun karba a cikin sunan fansar satar da ke ta karuwa a cikin yankuna daban-daban da ke arewacin Najeriya. A cikin 'yan makonnin nan dai an rika kallon sakin daruruwa na kamammu a bangaren ofishin mashawarcin tsaron Najeriya.

Karin Bayani: Shin lokaci ya yi da 'yan Najeriya za su gane matakan kariya?

Nasir El-Rufai tsohon gwamnan jihar Kaduna a NajeriyaHoto: Yusuf Ibrahim Jargaba/DW

A wani abin da Abuja ke yi wa fassara ta samun nasarar tsaro a bangare na jami‘an tsaron Najeriya. To sai dai kuma wani zargin biya na kudaden fansa a bangaren tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jigo a adawa ta kasar Nasir El-Rufa'i dai na neman yamutsa hazo cikin kasar a halin yanzu. El-Rufa'i dai ya ce Abuja tana biyan kudin fansa kafin ceton kamammun.

Zargin da kuma ya bata ran Abuja da ta ce babu gaskiya cikin mafarkin na El-Rufa'i. Wata sanarwar da ofishin mashawarcin tsaron gwamnatin ta fitar dai ta ce Abuja ba ta biya ko sisi ba a kokarin sakin kamammun.

Yankin jihohin Zamfara da Sokoto da ma Katsina dai na zaman kan gaba cikin biyan kudin fansa, kuma ra'ayi yana rabe bisa batun kudin fansar a tsakani na kwararrun da ke kallon matsalar ta tsaro a cikin yankin. Bashir Mohammad Gatawa dai ya ce biri yana kama da dan Adam cikin hasashen na El-Rufa'i.

Zaben barkwanci

Basharu Altine Guyawa dai na sharhi cikin batun tsaro a yankin arewa maso yamma, kuma ya ce in har da akwai alamu na biyan kudin fansa to ya fi kama da can cikin jiha ta Kaduna a maimakon jihohin na Sokoto da Zamfara. Duk da hukuncin da ke da tsauri a kasar dai sannu a hankali ana kallon karuwar cin riba ta kudin fansa a jihohin da ke fuskantar tashi da lafawar rashin tsaron.

Batun tsaro da tattalin arziki dai daga na alamu na zaman kan gaba cikin baka ta siyasar Najeriya da ke dada zafi yanzu.