1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaPakistan

Pakistan: Sammacin kamo Imran Khan

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 23, 2023

Kotun yaki da ta'addanci a Pakistan, ta bayar da damar kama tshon firaministan kasar Imran Khan. Kafar yada labarai ta Ary News ta ruwaito cewa, umunin kama Khan na da alaka da zargin tayar da tarzoma.

Pakistan | Imran Khan | Firaminista
Tsohon firaministan Pakistan Imran KhanHoto: Mohsin Raza/REUTERS

Tshon firaministan Pakistan din Imran Khan dai, yanzu haka yana tsare bisa zargin cin-hanci, kuma tarzomar ta birnin Lahore da ke zaman birni na biyu mafi girma a kasar ta faru ne yayin zanga-zangar adawa da kama shi kan zargin cin-hancin a watan Mayu na wannan shekara. Sai dai Khan ya musanta duka zarge-zargen biyu da ake masa.