1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin kasashe fursunoni a Burkina Faso

Suleiman Babayo ATB
April 20, 2020

Ana zargin jami'an tsaro Burkina Faso da halaka fursunoni 31 da aka kama bisa laifin ta'addanci yayin da kasar ke ci gaba da samun tashe-tashen hankula na tsegeru masu kaifin kishin Islama.

Mauretanien Soldaten des Tschad beim Training
Hoto: picture-alliance/ZUMA Wire/S. Lewis

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta zargin jami'an tsaron Burkina Faso da halaka fursunoni 31 wadanda aka kama ranar 9 ga wannan wata na Afrilu a garin Djibo lokacin samamen yaki da ta'addanci.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta ce ta yi magana da shaidun gani da ido 12 wadanda suka shaida abin da ya faru. Ana kyautata zaton mutanen da abin ya shafa kabilu ne na wasu makiyaya. Kungiyar ta Human Rights Watch ta nemi gwamnatin Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka ta yi binciken bisa lamarin da ke zama laifin yaki.

Mutane da dama sun halaka sakamakon hare-haren tsagerun masu kaifin kishin addinin Islama a kasar ta Burkina Faso tun daga shekara ta 2017.