Zargin juna a Ukraine
November 6, 2014Sojojin gwamnati a kasar Ukrainian sun musanta zargin da 'yan awaren gabashin kasar da ke goyon bayan Rasha suka y musu na kaddamar da sababbin hare-hare a kansu. Dakarun na Kiev dai sun ce har yanzu suna aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma tsakaninsu da 'yan awaren. Tun dai a watan Satumbar da ya gabata ne bangarorin biyu suka cimma yarjejeniyar tsagaita wutar, sai dai a 'yan kwanakin ne suna nunawa juna yatsa inda ko wanne bangare ke zargin dayan da karya ka'idojin yarjejeniyar. Tun da fari dai mataimakin Firaminstan yankin gabashin Ukraine din da suke kira da Tarayyar Al'ummar Donetsk ya yi zargin cewa dakarun gwamnatin Kiev sun kaddamar da sabon yaki a yankin gabashin kasar. A hannu guda kuma sojojin Ukraine din sun bayyana cewa an kashe dakarun soja uku a arangamar da suka yi da 'yan awaren.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu