'Yan adawa na barazanar kaurace wa zabe a Nijer
November 4, 2015A jamhuriyra Nijer a yayin da ake kasa ga watanni huku da a fara zabubukan kasar wata takaddama ce ta barke tsakanin bangarori daban-daban na siyasar kasar da ma masu ruwa da tsaki a fannin shirya zabe kan batun kundin rijistar sunayen masu zabe. Tuni 'yan adawa suka kalubalanci sabon kundin suna masu cewar koda hukumar zabe ta damka wa gwamnati shi ba za su kuskura su je zabe da shi ba muddin ba'a yi masa ingantaccen bincike ba, ganin irin yadda kundin yake tattare da kura-kurai.
A ka'idance dai kundin rijistar sunayen masu zaben tun a ranar 31 ga watan jiya ya kamata a ce a damka wa hukumar zabe shi domin amfani da sabon kundin a sabbin zabubukan kasar da za ta yi a tsakiyar watan Fabrairu na sabuwar shekara, sai dai tun ba'a kai ko ina ba kundin yake shan suka daga bakin rukunoni daban-daban na kasar cikinsu har da 'yan adawa da suka nuna cewar kura-kuran da kundin ya kumsa na daga cikin wasu sabbin dubarorin jam'iyyar da ke mulki na shirin kitsa mugudin zabe a sabuwar shekara mai kamawa.
A cewar Alhaji Lawali Mahamane Leger yarda da kundin rijistar zaben a yanzu har ma su je zabe na tamkar kai kansu ne mahalaka domin faduwa zabe a shekarar 2016 mai zuwa.
"Baya yuwa ace an rubuta sunan mutum tabbas ka rubuta sunanka sai a ce sunan ka bai fito ba, sannan ma tun daga farko basu yi wa tsarin bayyana sunayen jama'a biyayya ba ne na cewar inda a ka rubuta sunanka kamata ya yi ka same shi a wannan wurin, sai ka ji sunan ka wani wuri kamar misalin Bermo na jihar Maradi da na sani, sunayen 'yan Bermo sai a ka same su a Damagaram, ba yadda za'ayi mu 'yan adawa mu dauki hadarin amince wa wannan kundin tsarin rijistar sunayen masu zabe, bamu amince ba, idan ba'a sake su ba muka je zabe to duk abunda ya samemu mu muka ja".
Sai dai da take mayar da martini ga kalamun jam'iyyar PNDS tarayya mai mulkin kasar ta bakin kakakinta Malam Mohammed Moussa cewa ta yi hankalinta kwance yake game da duk wasu zarge-zargen magudi da 'yan adawar kasar ke yi daman dai sun ga alamun tamkar ba sa kai labari ne suke neman su shafa wa jam'iyyar ta PNDS Tarayya da ke mulki kashin kaji.
"Abin da muke so shi ne mu bayyana wa duniya da cewar lalle koda da a kwai matsaloli muna iya zama mu yi aiki tare domin zuwa zabe wanda Allah ya bai wa mulki mu bi shi, mu mutanenmu da muka sa a cikin wannan hukumar ta tsara kundin rijistar sunayen masu zabe bamu ce masu su yi magudi ba, bamu neman magudi ko guda kuma shugaban kasa da kanshi ya fada".
Anata bangare itama hukumar ta CEFEB mai kula da aikin rubuta sunayen masu zaben ta nisanta kanta da duk wasu abubuwa na amfani da ita domin shirya magudi.
Kimanin 'yan Nijer Miliyan bakwai da dubu dari biyar ne hukumar ta CEFEB ta ce ta rubuta a cikin sabon kundin rijistar sunayen masu zabe domin ba su damar jefa kuri'a, sunayen da 'yan adawar suka kalubalanta da cewar wasu wuraren anyi a aringizon jama'a.