1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zargin magudi a Jamhuriyar Nijar

Gazali Abdou Tasawa
December 22, 2020

A Jamhuriyar Nijar jam'iyyar MNSD Nasara ta zargi abokiyar kawancen mulki jam'iyyar PNDS Tarayya bisa zargin tafka magudi a zaben kananan hukumomi a wasu yankunan kasar.

Wahlplakat für Seini Oumarou Niger
Hoto: DW/M.Kanta

A Jamhuriyar Nijar jam'iyyar MNSD Nasara Nasara abokiyar kawancen mulki da jam'iyyar PNDS Tarayya ta yi zargin tafka magudi da ma kwace akwatinan zabe a zaben kananan hukumomi a wasu yankunan kasar. Ta sanar da haka ne a wata sanarwa da ta fitar inda ta sha alwashin hana kowane dan takara lashe zaben shugaban kasa tun a zagayen farko.

Ko da shi ke cewa a sanarwar da ta fitar ba ta fito fili karara ta kira sunan jam'iyyar da take zargi da aikata magudi da kwace akwatinan zabe a zaben kananan hukumomin ba, amma dai ta yi gugar zana ta yadda za a iya fahimtar korafinta na a kan abokiyar kawancenta ce a mulki wato jam'iyyar PNDS Tarayya.

Jam'iyyar ta MNSD Nasara ta kuma sha alwashin ganin babu wani dan takara da zai lashe zaben shugaban kasa tun a zagayen farko kamar yadda wasu ke ikirari daga bangaren jam'iyya mai mulki da ma kuma magudin da ake gani na wakana tun a zaben kananan hukumomi.

Jam'iyyar ta MNSD Nasara ta ce wakilinata wadanda suka yi kokari hana aikata magudin an lakkada masu dan karan duka. Jam'iyyar ta MNSD Nasara ta ma zargi cewa a wurare da dama an aikata magudin da aringizon kuri'u a bisa lamuncewar ko hadin bakin wasu shugabannnin hukumar zaben mai zaman kanta. Kokarin da muka yi na jin ta bakin hukumar zaben ya ci tura inda aka ce da mu mambobinta na cikin taro. Sai dai daga bangaren jam'iyyar PNDS Tarayya ta bakin kakakinta Malam Asumana Mahamadou ta mayar da martani inda ta musanta zargin.

Yanzu haka ana jiran hukumar zabe ta bayyana kammalallen sakamakon zaben kananan hukumomi, wasu alkalumma na bayan fage na nuni da cewa jam'iyyar PNDS Tarayya ta yi wa sasuran jam'iyyun tazarar da ta wuce kima, lamarin da ya sanya yanzu haka jam'iyyun na adawa da na bangaren masu mulki ke kan hanyar kafa wani sabon kawance wanda ke da burin hada kai domin kalubalantar Bazoum Mohamed a zaben shugaban kasar na ranar Lahadi mai zuwa.