1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin magudi daga kundin masu zabe a Nijar

Mahaman KantaOctober 30, 2015

Shugabannin jam'iyun adawa na ARDR sun sanar da bankado wani shirin magudi a kundin rajistan masu zabe na kasar, wanda suka ce hukumar kula da rajistan masu zabe wato CFEB.

Hoto: DW/M. Kanta

A cikin wani taron manema labarai ne dai da 'yan adawan suka kira a birnin Yamai suka sanar da wannan labari kamar yadda Sani malam Maman mataimakin shugaban jam'iyyar Moden Lumana Afirka ya yi tsokaci a gaban manema labarai...

Hoto: DW/M. Kanta

" A dauki mutun daga wata jiha a kai wata jiha, ko a dauki sunayan mutane na wata karamar hukuma ga baki daya a kai su wata jiha, kuma wannan matsala ta shafi dukannin jihohin kasar. Ga musali jihar Tillabery babu mazabu wajan 300, a jihar Tahoua babu mazabu wajan 400, a Agadez an gano babu mazabu a kalla 15, jihar Dosso babu mazabu a kalla 50, sannan kuma mutane da dama sun tabbata an yi raijistan su amma kuma babu sunayansu."

Sai dai a bengaran jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya wannan korafi babu wata hujja a cikin shi, domin kuwa a cewar Aboubakar Sabo wakilin wannan jam'iyya a hukumar kula da rajistan masu zabe ta CFEB ya yi na shi tsokaci...

Hoto: DW/T.Mösch

"Su masu wadannan maganganu ana iya cewa har yanzu ba su san manufar fiddo da jerin sunayan mutane a yanzu ba, domin da ma ana yin haka ne don mutane su gano kura-kuran da ke ciki domin a gyara, shi ya sa ba a fitar da katocin zabe ba kai tsaye. Kenan kididdigar da aka yi ta wajan mutane miliyan bakoye har da wajan dari biyar (700.500.000) wadanda suka yi rijista, don haka a dole ne a samu kura-kurai wajan buga sunayansu a konfuta."

Hadin gwiwar jam'iyyun adawar dai sun sanar cewa ba komai ba ne illa kawai wani salo na magudi domin cin zabeko ta halin kaka, inda suka ce sam ba za su yarda da wannan aika-aika ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani