Tuhumar cin zarafin yara a Malesiya
September 12, 2024Hukumomin kasar Malesiya sun zurfafa binciken da suke yi kan wata ficecciyar kungiyar addinin Islama ta kasuwanci, kwana guda bayana 'yan sanda sun ceto yara fiye da 400 da ake zargin ana lalata da su, a gidajen da kulawa da kungiyar take tafiyar da su. Hukumomi suna gudanar da bincike kan cibiyoyin ba da ilimi na kungiyar, domin gano irin dokokin da kungiyar ta karya.
Ita dai kasar Malesiya da ke dauke da galibin mabiya addinin Islama tana gudanar da harkokin mulki mai ruwa biyu na addinin Islama da kuma tsarin da babu ruwansa da addini. 'Yan sandan kasar sun kai farmakin hadin gwiwa lokaci guda a sassan kasar kan cibiyoyin wannan kungiya ta addinin Islama da ta yi fice inda aka ceto yara maza da mata da ake zargi ana cin zarafi, tare da kama fiye da mutane 170 da suka hada da malaman addinin Islama. Mai magana da yawun kungiyar ya yi alkawarin ba da hadiun kai ga hukumomi kan binciken da ake yi na halin da ake ciki.
Tuni asusu kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya nuna kaduwa da abin da ya faru a kasar ta Malesiya, sannan ya bukaci hukumomin Malesiya su bai wa yaran kula lafiyar jiki da na kwakwalwa.