Zargin Musharraf da aikata babban laifi
November 17, 2013Kasar Pakistan ta bayyana cewar za ta gurfanar da tsohon shugaban kasa Pervez Musharraf gaban kuliya bisa zarginsa da ta ke yi da cin amanar kasa. Ministan cikin gidan Chaudry Nisar Ali Khan ya nunar a birnin Islamabad cewa Musharraf ya kafa dokar ta baci a shekara ta 2007 a daidai lokacin da alkalai ke kalubalantar mulkinsa.
Wannan dai shi ne karon farko da aka zargi tsohon shugaban kasa da irin wannan laifi a Pakistan, duk da juye-juyen mulki da ta fi fama da su a shekarun baya. Idan ko an same Musharraf da wannan laifi, za a iya yanke wa tsohon shugaban na Pakistan hukunci rai da rai.
Wadanda suke nakalci kabli da ba'adi na harkokin siyasar wannan kasa suna ganin cewa gurfanar da Musharraf zai sake tayar da tsohon tsumi da ke tsakanin gwamnatin da ke ci a yanzu da kuma sojojin kasar. Idan za a iya tunawa Pervez Musharraf ne ya hambarar da gwamnatin firaminista na yanzu wato Nawaz Sharif a shekarar 1999. Sai dai Musharraf ya katse gudun hijira da ya ke yi domin ya samun damar tsayawa a zabukan gama gari da za su gudana a watan Mayu mai zuwa idan Allah ya kaimu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar