1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin Shell da gurɓata muhali a Najeriya

October 11, 2012

Wata kotun Netherlands na sauraron ƙarar da wasu 'yan Najeriya suka shigar a gabanta, bisa zargin kanfanin mai na Shell da laifin gurɓata muhalli a yankin Neija Delta.

Hoto: AP

Shigar da ƙa'rar da ta shafi gurɓata muhalli a yankin Neija Delta mai arziƙin man fetur da ke tarayyar Najeriya dai na ɗaukar hankali ne saboda irin tasirin da shari'ar za ta yi akan harkokin manyan kanfanonin man fetur a duniya - ciki harda da kanfanin Shell, wanda ke da cibiyar sa na ƙasa da ƙasa a birnin the Hague, inda nanne ake gudanar da shari'ar, wadda kuma wasu 'yan Najeriya huɗu da suka ƙunshi manoma da masunta tare haɗin gwiwar wata ƙungiyar da ke fafutukar kare muhalli a duniya suka shigar domin neman haƙƙinsu.

A cewar masu gabatar da ƙa'rar dai mala'lar man fetur a yankunan su - har sau ukku a shekara ta 2004 da 2005 da kuma 2007, sun kawo cikas ga sana'oin da suke gudanarwa domin ciyar da iyalansu.

Neman Shell ya biya diyya

Mutanen suka ce fashewar bututun man fetur na Shell da kuma ayyukansa na haƙo man fetur ne suka gurɓata muhallan na su, abinda yasa suke neman kotun ta tilastawa kanfanin biyan su diyya.

A cewar Geert Ritsema wani mai fafutuka a ƙasar ta Netherlands, wanda ke cikin jerin waɗanda suka gabatar da ƙa'rar sakacin da kanfanin Shell ke yiwa rayuwar mazauna yankin Neija Delta da ke Najeriya ba mai karɓuwa bane:

Hoto: AP

"Kanfanin Shell na yin baki biyu a yanda yake tafiyar da harkokin sa a Najeriya saɓanin a Turai. A Turai ba zai taɓa yiwuwa kanfanin mai ya gurɓata gonar manomi kuma ya kyale filin haka na tsawon shekaru ba, amma a Najeriya sukan yi hakan ba tare da fuskantar wani hukunci ba, abinda yasa kanfanonin ke nuna halin ko oho ga matsalar."

Wani sakamakon binciken da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gudanar dai na nuni da cewar tun kimanin shekaru 50 da suka gabata ne harkokin haƙo man fetur ke la'la'ta muhalli a yankin Neija Delta, wanda kuma a cewar rahoton, zai ɗauki kusan shekaru 30 gabannin sake farfaɗo da yankunan da mai ɗin ya lalata.

Dacewar sauraron shari'ar a Turai

Sai dai kuma masana harkokin shari'ah na tsokaci game da dacewar wata kotun Turai ta saurari wani laifin da aka aikata a wajen nahiyar, abinda yasa Liesbeth Enniking ƙwararriya a harkar shari'a da ke jami'ar Ultrecht a ƙasar Netherlands bayyana cewar akwai ƙalubalen da ke tattare da shari'ar:

"Galibin shaidun da za'a gabatarwa kotu dai ba sa hannun masu shigar da ƙara. Suna hannun gaggan waɗanda ke kare kansu ne. Alas misali: Me ya janyo malalar man fetur ɗin? Me ya faru? Shin zagon ƙasa ne ko kuma rashin gyara ne? Wani mataki ne kanfanin Shell ya ɗauka bayan malalar mai ɗin, kuma menene ƙarfin ikon da kanfanin Shell ke dashi ta fuskar kula da harkokin bututun man fetur a Najeriya."

Ƙwararriyar ta ce sauraron shari'ar a ƙasar Netherlands na da tasiri ta fuskar cewar kotun na da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi rassan kanfanin Shell da ke ƙetare ba wai kawai wanda ke Turai ba. Sai dai kuma ta ce akwai yiwuwar kanfanin ya nemi sansantawa a wajen kotu:

Hoto: Mazen Saggar/UNEP

"Manyan kanfanonin ƙasa da ƙasa za su iya rungumar hanyar sasantawa a wajen kotu idan suka fahimci cewar ba za su yi nasara a shari'ar ba, domin gudun tasirin hukuncin da ba zai yi musu daɗi ba ga harkokin su."

Duk ƙoƙarin da DW ta yi na jin martanin Shell game da shari'ar birnin na The Hague ya ci tura. 

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita:  Mohammad Nasiru Awal