Human Rights Watch ta zargi sojan Burkina
July 8, 2020Talla
A cikin wani rahotonta kungiyar ta wallafa kungiyar ta ce an samu wasu kaburburan jama'a wadanda aka kashe haka suddan ba tare da yi masu shara'a ba a yankin Djibo na arewacin Burkina Faso 180, bayan ta gudanar da bincike da jin ra'ayin jama'a, inda ta ce mutanen yankunan da kansu tare da agajin soja suka binne mamatan hade a cikin kaburbura a watanin Maris da Aprilun da suka gabata.
Ba tun yau ba dai ake zargin jami'an tsaron Burkina Faso da aikata kisan jama'ar da basu san hawa ba su san sauka ba a yakin da suke da 'yan ta'adda kan iyakokin kasar masu makwaftaka da Mali da Nijar.