1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Zargin take hakkin dan Adam

Mimi Mefo BB/FDLM
November 21, 2024

Shararren mawakin kasar Malin nan Salif Keita ya nuna goyon bayansa a fili ga gwamnatin mulkin sojan kasar, a daidai lokacin da masu sukar lamirin gwamnati ke kara nuna damuwa kan take hakkin dan Adam.

Mali | Kanal Assimi Goïta | Soja | Mulki | Danniya
Jagoran gwamnatin mulkin soja ta Mali Kanal Assimi GoïtaHoto: OUSMANE MAKAVELI/AFP/Getty Images

Fitaccen mawakin na kasar ta Mali, Saif Keita dai ya yaba da salon mulkin sojojin da suka yi juyin mulki tare da yin watsi da zargin da ake musu na take hakin dan Adam. Wannan matsayar ta mawakin ta haifar da zazzafar muhawara a kasar, kasancewar ana ganin gwamnatin mulkin sojan da gudanar da mulkin danniya. To sai dai Keita ya shaidawa DW cewa, babu wani zabi da ya ragewa 'yan Mali da ya wuce mulkin soja domin ceto kasar daga cikin kangin da ta fada na rikice-rikicen siyasa da kuma tsaro. Sai dai duk da kariyar da mawakin ya bai wa sojojin da ke mulkar kasar kan zargin kama-karya, kungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma masana suna da ja a kan wannan hakan kasancewar sun yi wa gwamnatin bakin fenti. Aguibou Bouare shi ne shugaban Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasar, ya ce duk wani dan kasa ciki har da Keita na da 'yancin fadin albarkacin bakinsa sai dai kuma a rika fadin abun da yake a zahiri.

Mali: Sojojin Jamus za su kula da batun kare hakin dan Adam

02:09

This browser does not support the video element.

Shima dai tsohon ministan shari'a na kasar Mamadou Ismaila Konate ya soki irin yabon da Keita yake yi wa majalisar mulkin sojan, inda ya bayyana shi a matsayin dan abi yarima a sha kida. Ya nunar da cewa ta'asar da ake ci gaba da yi da kuma murkushe 'yan adawa, wata babbar shaida ce ta mulkin danniya. Masu sharhi a kasar na ci gaba da kafa hujja da abubuwan da ke faruwa a MAlin a baya-bayan nan, na yadda gwamnati ke kokarin rufe bakin 'yan adawa. Wannan yabon da gwmnatin mulkin sojan Mali ke samu daga bakin mawakin dai, na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke kara fadawa cikin rikicin siyasa. Shugaban majalisar mulkin sojan Malin Kanal Assimi Goïta  ya tsige firaministan kasar Choguel Kokalla Maiga tare da mukaraban gwamnatinsa, matakin da ke zuwa kwanaki kalilan bayan da firanministan ya caccaki gwamnatinsa kan rashin cika alkawarin da ta dauka na gudanar da zabe domin mayar da kasar kan tafarkin dimukuradiyya.