Zargin yin amfani da addini domin cimma burin siyasa a Najeriya
January 8, 2014Yakin cacar bakan da ke faruwa a tsakanin jam'iyyun biyu na PDP da APC da a kullum ke kara zafafa fagen siyasar Najeriyar, a yanzu sannu a hanakali ya fara tashi daga abin da ake wa kallon adawa ce ta siyasa kawai ya zuwa ta kokarin kaiwa ga madafan ikon kasar ko ta halin kaka, musamman ganin cewa kasar na kara shiga cikin jajiberin babban zaben da za'a gudanar a shekara mai zuwa.
Duk da cewa akan danganta cece-kuce a fagen siyasa a matsayin gishiri ga dimokradiyya domin yin shiru kan sa a ji fagen ya yi tsit. To sai dai sabon salon da wannan lamari ke dauka na kokarin cusa addini a cikin siyasar Najeriyar, inda jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa jam'iyyar adawa ta APC na kokarin cusa salo irin na jam'iyyar ‘yan uwa Musulmi ta kasar Masar, wacce har yanzu hayakin rikicin da ya turnike a dalilinta bai gama kwantawa ba. Tuni dai jam'iyyar APC ta mayar da martani. Injiniya Buba Galadima na cikin dattawan wannan jam'iyya, kuma ya ce yana cike da mamakin abin da ya kira yarfan siyasa.
‘'Abin na bani mnamaki, in banda abin mamaki yaushe PDP za ta yi wannan Magana. Ai abin da yake afkuwa yarfe ne kurum irin na siyasa don su basu yarda da dimokradiyya ba, basu bar dan Najeriya ya zabi abin cda yake so ba. Don haka na yi mamaki kwarai da gaske cewa wannan Magana ta fito daga bakin PDP.''
Ra'ayin 'yan Najeriya akan cusa addini cikin harkar siyasa
Ga mafi yawan al'ummar Najeriya kan yi kallon cewa, cusa addini a siyasa wata yaudara ce kawai, domin sai a lokacin zabe ne ake nunawa talaka cewa akwai irin wannan bambanci.
Wannan ya sanya Dakta Sadeeq Abba, masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja, babban birnin Najeriya kashedin cewa, akwai bukatar yin taka tsan-tsan.
‘'Cusa addini a cikin siyasa, ba a Najeriya kadai ba amma a duk duniya fitina ce. In aka duba tarihin Najeriya a lokutan baya mun fuskanci fitintinu da yawa, in ka duba za ka ga cewa dalilin hakan shi ne ‘yan siyasa sun cusa addini a cikin siyasa, amma fa ba laifin 'yan siyasan bane, wannan laifin talaka ne wadanda sai a ajiye su a kullum sai zabe ya kusa, sai a fito a nuna masu zancen addini. Don haka kada talakawa su yarda a yaudare su da wannan zancen addini.''
Gargadi akan bukatar zaman lafiya da juna
To sai dai nazarin inda aka fito a irin wannan batu da a lokutan baya ya jefa Najeriyar cikin mawuyacin hali, ya sanya Malam Muhammad Awwal Abubakar Bayyana cewa tunda an gina siyasar Najeriya akan tsarin mulki ne, to, kamata yayi 'yan kasar su mayar da hankali akan zaman lafiya da junansu.
Duk da cewa babu yadda za'a iya kawar da adawa a tsakanin jamiyyun da ke kara neman kafuwa a kasar da ke fuskantar zabe, to sai a yanzu a zamanace ake yinta saboda ci gaban da aka samu, abin da ya sanya bukatar bin ka'idojin dimokradiyyar na neman samun nasara ta amfani da karfin kuri'u.
Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Saleh Umar Saleh