1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zawarcin jam'iyyu don kafa kawance

Zainab Mohammed Abubakar MNA
September 25, 2017

CDU da CSU da FDP da kuma The Greens a cikin gwamanti - shin zai yiwu? Angela Merkel na kokarin janyo SPD a ciki.

Deutschland Bundestagswahl Merkel PK
Hoto: Reuters/F. Bensch

Yanzu haka ya zama wajibi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi zawarcin jam'iyyun da za ta yi kawance da su domin kafa gwamnatin hadin kan kasa. Kuma bisa ga dukkan alamu jam'iyyar masu ra'ayin sassauci ta Free Demokrat wato FDP da a baya ta yi kawance da ita da kuma masu aikidar kare muhalli wato The Greens, su ne kawayen zawarcin jam'iyyar ta CDU. Sai dai akidar kawar kawancenta wato CSU da ta masu fafutukar kare muhallin sun yi hannun riga. Amma Merkel ta ce komai mai iya faruwa ne. 

"Ba zan iya fayyace komai ba a yanzu, kuma ba zan fidda zato ba. JamI'iyun CDU da CSU za su goyi bayan duk abin da ke da muhimmanci. Abin da ke da muhimmanci a gareni shi ne, za mu samu karin amfani da Turai, amma akwai bukatar karin damarmaki da samar da aikin yi. Wajibi ne hakan ya yi tasiri wajen karfafa Turan. Ba wai a yi kalamai masu dadi kawai ba, amma mu tabbatar da hakan a aikace."

Shugaban FDP Christian LindnerHoto: Reuters/W. Rattay

Jam'iyyar FDP da ta samu nasarar komawa majalisar dokokin Jamus ta Bundestag bayan hutun shekaru hudu ta samu nasarar lashe kashi 10.7 cikin 100 na kujeru a majalisar. Ta ce shiga gwamnatin hadaka da CDU na nufin sauya tafiya a lamuran siyasar kasar. Angela Merkel ta shiga gwamnatin hadaka da FDP a lokacin wa'adin mulkinta na biyu tsakanin 2009 zuwa 2013, kafin ta rasa wakilci a majalisa shekaru hudu da suka gabata. Christian Lindner shi ne shugaban jam'iyyar FDP na kasa.

"Mu na muradin sauyin alkibla a siyasance. Idan ba mu cimma burinmu ba kuwa, za mu gwammace taka rawa a matsayin 'yan adawa. Domin babu abin da zai fi muni kamar sabuwar gwamnati mai launuka dabam-dabam, ta ci gaba da yin abin da gwamnati mai bakin launi da ta shude ke yi."

Hoto: picture-alliance/dpa/F. Rumpenhorst

Kawancen da ake masa lakabi da "Jamaica Coalition" saboda launukan jam'iyyun wato CDU mai baki da FDP mai dorawa da Greens mai kore sun yi daidai da launukan da ke kan tutar kasar Jamaica.

A nata bangare jam'iyyar masu fafutukar kare muhalli wato The Greens ta ce za ta yi watsi da duk wani abu da zai kawo raba kan kasa, ko batun nuna wariya ko akidar kyama a cikin majalisar dokokin da za a kafa. A taron manema labarai a birnin Berlin, ra'ayin shugabannin jam'iyyar biyu Katrin Goering-Eckardt da Cem Özdemir ya zo guda na cewar ba za su bar jam'iyyar masu kyamar baki ta AfD da ta zama na uku a yawan kujeru a majalisar, ta mamaye majalisar da akidarta ba.

Cem Özdemir da Katrin Göring-Eckardt na jam'iyyar The GreensHoto: Reuters/W. Rattay

Sai dai suna masu ra'ayin cewar ya dace a shawo kan matsalar da ta janyo wa jam'iyyar gagarumar nasarar da ta samu. Dangane da yiwuwar amincewa da shiga gwamnatin hadaka kuwa ga abinda Cem Özdemir ke cewa.

"Muna muradin jagorantar tattaunawa mai ma'ana, sai dai hakan ya danganci abubuwan da za a cimma matsaya a kai dangane da yarjejeniyar. A dangane da lokaci na farawa, ba batu ne na mu kadai ba, amma har da sauran bangarorin, ta yadda za su yi nazarin batutuwa tsakaninsu, musamman idan aka yi la'akari da sakamakon CSU, kan wakilanta da ke majalisa."

Duk da cewar Merkel ta mika goron gayyata ga jam'iyya ta biyu mafi karfi ta SPD wadda ita ma ta yi asarar kujerunta da dama a zaben, a ta bakin babban dan takararta Martin Schulz a kai wannan tayi kasuwa domin sun gwammace yin adawa a cikin majalisar.