1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan siyasa na fafutukar neman shugabanci

May 15, 2019

A cikin makon gobe ne za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin na Kungiyar Tarayyar Turai ta EU. Kimanin wakilai 751 ne dai masu kada kuri'a a kasashen da ke cikin kungiyar ta EU za su zabe domin girka majalisa ta 9

Deutschland | Wahlarena zur Europawahl | Manfred Weber (l, EVP) und Frans Timmermans (SPE)
Hoto: picture-alliance/dpa/Bildfunk/R. Vennenbernd

 Abu mafi muhimmanci da za a fi mayar da hankali da zarar an kammala zaben shi ne fidda mutumin da zai jagoranci kungiyar kuma tuni masu sha'awar wannan matsayi suka fara zawarcin kujera.

Bisa al'ada dai da zarar zabe ya kammala, sabbin 'yan majalisar EU din kan dukufa ne wajen ganin sun zabi wanda zai jagoranci kungiyar ta EU kuma mafi akasari jam'iyyar da ke da rinjaye ce tare da hadin kan shugabannin kasashen da ke zaman mambobi na kungiyar kan fitar shugaban. A kan gabatar da sunan dan takarar da ake son ya jagoranci EU din ne gaban 'yan majalisar dokokin don neman sahalewarsu ko da dai bai zama wajibi a bi wannan tsari ba. Tuni dai sunayen fitattun 'yan siyasa da ke sha'awar wannan matsayi suka fara bayyana tun ma gabannin yin zaben na 'yan majalisar.

Guda daga cikin masu zawarcin wannan kujera dai shi ne Manfred Weber, dan jam'iyyar nan ta CSU da ke jihar Bavaria a nan tarayyar Jamus. Da dama sun yi mamakin fitar sunan duba da yadda ya baya ya yi kaurin suna wajen caccakar tsarin da EU din ke kai sai dai daga baya ya sassauto daga wannan matsayi da yake kai kuma 'yan shekarun da ya kwashe a majalisar dokokin EU din ya yi aikace-aikace da dama wanda da dama suka jinjina masa har ma hakan ya sanya shi kasancewa shugaban kungiyar 'yan majalisa na na jam'iyyar EPP wanda dama ke ganin hakan ka iya taimaka masa wajen shan kan 'yan majalisar su zabe. Wani abu har wa yau da ka iya taimaka masa shi ne fafutukarsa wajen ganin an samar da hanya shigar 'yan gudun hijira EU bisa ka'ida.

Manfred Weber-Dan takarar majalisar TuraiHoto: Getty Images/AFP/L. Gouliamaki

 

"Manfred Weber kenan yake cewar killace kan iyakokinmu abu ne mai muhimmanci idan ana magana ta karbar bakin haure. Kamata ya yi a ce kasashen EU ne ke yanke huknci kan wanda zai shiga Turai a matsayin dan gudun hijira ko dan cira ba wai masu safarar mutane be. Wannan abu ne da ya kamata a yi aiki a kansa don ganin ya tabbata".

 

Baya ga Weber, wani dan takarar da ake ganin za a ja zare da shi ne Frans Timmermans wanda a yanzu haka shi ne mukaddashin shugaban Kungiyar EU din kana shugaban kungiyar 'yan majalisa na jam'iyyar Socialist. Gabannin zuwansa majalisar da ma hawansa wannan matsayi, Timmermans wanda dan asalin Netherlands ne, ya rike mukamai a kasarsa wanda suka hada dan majalisa da minista. Mutum ne da ya yi fice a Turai sannan yana jin harsuna. Timmermans ya yi fice wajen fafutuka ta ganin tsaftace harkar karbar 'yan gudun hijira sannan mutum ne da ya yi tsayin daka wajen ganin an dauki kwararan matakai na alkinta muhalli har ma ya bada shawar sanya haraji kan masu fidda hayakin da ke gurbata muhalli.


"Wannan haraji abu ne mai kyau sai dai kuma idan aka dube shi ta wata fuskar za a ga cewar zai haifar da hauhawar farashi na albarkatun man fetur, hakan kuma zai iya kasacewa babban kalubale ga masu karamin karfi a tsakanin a'umma".

Margrethe Vestager-Kwamishinar Turai Hoto: Reuters/F. Lenoir

 

Margrethe Vestager ma dai guda ce daga cikin 'yar majalisar da ake ganin za a fafata da ita wajen neman kujerar shugabancin kungiyar ta EU. 'Yar asalin kasar Denmark, Vestager ta taba kasancewa minista kasarta kuma irin kwazonta da jajircewa kan aiki musamman ma sanda take rike da ministan cikin gida a kasarta ya sanya 'yan siyasar Turai da dama ke ganinta da kima. Tuni dai Ms. Vestager ta fara zawarcin wanna kujera idana a jiyota tana cewar loakci yayi da mace za ta kasance shugabar EU.

To baya ga wadannan 'yan takara akwai karin wasu wanda suka hada da Jan Zahradi dan Jamhuriyar Chech da Nico Cue daga Slovenia sai kuma Ska Keller dan Jamus wanda shi ne ne dan takara mafi kankantar shekaru a cikin masu zawarcin shugabancin kungiyar.