Zazzabin dengue ya hallaka mutane a Burkina Faso
October 21, 2023![Nau'in sauron da ke haddasa cutar dengue](https://static.dw.com/image/66697248_800.webp)
Talla
Ma'aikatar ta ce ana zargin fiye da mutane 50,000 ne suka kamu da cutar yayin da kimanin 214 suka mutu sanadiyar cutar da ake samu daga sauro a wannan shekarar. An dai samu bullar cutar ce a babban birnin kasar Ouagadougou da kuma Bobo Dioulasso. Alkalumma sun yi nuni da cewa, cutar zazzabin dengue na kashe mutane a kalla dubu 20 a duk shekara a duniya.
A wannan watan ne dai Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi cutar ka iya zama babbar barazana ga wasu kasashen nahiyar Afirka.