1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta bukaci karin taimako daga Birtaniya

Suleiman Babayo MAB
July 19, 2024

Shugaba Volodymyr Zelenskiy na kasar Ukraine ya yi jawani ga sabuwar majalisar ministocin Birtaniya karkashin sabon Firaminista Keir Starmer game da taimakon kasarsa kan yakin da take fuskanta.

Birtaniya, London 2024 | Firaminista Sir Keir Starmer na Birtaniya da Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine, gami da Ministan Tsraon Birtaniya John Healey
Firaminista Sir Keir Starmer na Birtaniya da Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine, gami da Ministan Tsraon Birtaniya John HealeyHoto: Richard Pohle/AP Photo/picture alliance

A wannan Jumma'a Shugaba Volodymyr Zelenskiy na kasar Ukraine ya gabatar da jawabi ga majalisar ministocin kasar Birtaniya karkashin sabon Firaminista Keir Starmer, game da matsayin Birtaniya na ci gaba da taimakon Ukraine kan kutsen da take fuskanta daga Rasha.

Karin Bayani: Sabon firaminista ya yi alkawarin sake gina kasar

Shugaban na Ukraine ya samu gagarumar tarba daga majalisar ministocin ya kuma jaddada kiran da yake yi wa kasashen Yammacin Duniya na amince da amfani da makamansu wajen kai harin ramuwa cikin Rasha. Ita dai Biratniya ta kasance sahun gaba na masu goyon bayan Ukraine tun lokacin da ta fuskanci kutse daga Rasha a shekara ta 2022.