1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Zelensky da Mitsotakis na Girka sun tsallake rijaya da baya

March 7, 2024

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da Firaminista Kyriakos Mitsotakis na Girka wanda yake ziyara a Ukraine sun tsallake rijaya da baya biyo bayan wani harin makami mai linzami da Rasha ta harba a gabar tekun Odessa.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy da Firaiministan Girka Kyriakos Mitsotakis a wata ganawa a birnin Athen na Girka
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy da Firaiministan Girka Kyriakos Mitsotakis a wata ganawa a birnin Athen na GirkaHoto: Petros Giannakouris/AP Photo/picture alliance

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da Zelensky ke gudanar da wani rangadi a yankin na Odessa tare da Firaiministan Girka Kyriakos Mitsotakis, domin duba halin da tashar ke ciki wajen jigilar kaya a Bahar Aswad, inda shugabannin biyu suka bayyana lamarin a matsayin hari na ban mamaki.

Karin bayani: Jamus ta goyi bayan Jamhuriyar Czech na samar wa Ukraine makamai

Wani sojan ruwan Ukraine ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewa harin na Rasha ya hallaka mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.

Ukraine da Rasha na ci gaba da zafafa hare-haren da suka kaiwa duk da cewa Moscow na ci gaba da fadada kai farmaki Kiev, yayinda Ukraine din ke kukan karancin makamai na kare kan ta.

Karin bayani: Ukraine ta koka kan jinkirin zuwan tallafin ketare

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da Allahwadai kan harin na Rasha a kusa da shugabannin Ukraine da Girka, inda Firaiministar Italiya Giorgia Meloni ta yi kakkausar suka ga Rasha kan harin na Odessa.