Rasha: Ukraine ta yi wa Jamus godiya
October 26, 2022Talla
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gode wa shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier bisa ziyarar da ya kai kasar a ranar Talata. Zelensky ya isar da godiyarsa ga kasar Jamus kan taimakon da take ba su wajen kare kansu a yakin da Ukraine ke yi da Rasha.
To sai dai shugabannin biyu ba su ce 'uffan' ba a game da rashin fahimtar juna ta diflomasiyya da Zelenksy ya samu da Steinmeier, lamarin da ya hana shugaban kasar ta Jamus ziyartar Ukraine a watannin baya. To amma Steinmeier ya jinjina wa Zelenksy a bisa jagorancin da yake yi wa Ukraine a cikin mawuyacin halin da kasarsa ta tsinci kanta na yaki da Rasha.