1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Taron EU: Zelensky ya nemi karin tallafi

October 17, 2024

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai na ci gaba da taronsu na koli a birnin Brussels, wanda ya mayar da hankali kan yakin Rasha da Ukraine da sababbin manufofin tattalin arziki.

Tarayyar Turai  EU | Taro | Volodymyr Zelensky | Ukraine | Rasha
Taron koli na shugabannin kungiyar Tarayyar Turai EU a birnin Brussels na BeljiyamHoto: NICOLAS TUCAT/AFP

Manyan batutuwa guda uku ne suka kasance jigon taron shugabanni na EU, wanda ke zuwa a daidai lokacin da masu ra'ayin mazan jiya ke kara karfinsu a kasashen kungiyar mai mambobi 27. Yakin Rasha da Ukraine ya kasance babban batu da aka tafka muhawara a kai, inda bako na musamman Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine din ya sake jaddada neman karin tallafin makamai domin fuskantar dakarun Rasha tare kuma da nanata kudurin kasar na samun gurbi a kungiyar Tsaro ta NATo. Shugaba Zalensky ya kuma gabartar da wani shiri ga shugabannin kasashen EU 27 da kuma ministocin tsaron kasashen NATO 32, mai kunshe da manufofi guda biyar da suka shata dabarun samun nasara a yakin da kasarsa ke yi da Rasha. Ya ce ko da za a warware wannan rikici tsakanin kasashen biyu ta hanyar diflomasiyya, ya zama wajibi Rasha ta dandana radadin da al'ummar Ukraine ta ji a tsawon lokacin da aka kwashe ana yakin.

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, ya nemi karin tallafi daga EUHoto: Handout/UKRAINIAN PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/AFP

Sai dai da alamu a wannan karo ma da akwai wuya hakar Zalensky ta cimma ruwa 100 bisa 100, domin an jiyo sabon sakataren NATO na cewa za su ci gaba da taimakon Kiev da makamai amma sai ta jira kafin ta zama mamba a cikin kawancensu. Batu na biyu da ya mamaye taron na EU shi ne sababbin manufofin dakile bakin haure, watanni biyar bayan kungiyar ta sake samar da wasu dokoki. Sai dai kawunan kasashen sun rarrrabu kan sabuwar alkiblar da ake son dosa, inda Spaniya ta yi watsi da sabon tsarin da tuni Italiya ta fara aiwatar da shi na mayar da 'yan ci-rani zuwa wasu cibiyoyi da ke kasar Albaniya. Faransa kuwa ta nuna dari-dari a kan tsarin ne, yayin da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci da a sake yin nazari. Rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ya kasance jigo na uku a taron na birnin Brussels, a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke zafafa hare-hare ta sama a kasar Lebanon a dauki ba dadin da suke yi da kungiyar Hezbollah mai alaka da Iran. Ko da yake kasashen na da ra'ayoyi mabambanta a daukar fansar da Isra'ila ke yi kan harin Hamas na ranar bakwai ga watan Oktobar bara, amma dukkanninsu na karkafa fatan ganin an dakile barazanar yaduwar wannan rikici a fadin yankin tare da kawo karshen zubar da jinin fararen hula.

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani