Yakin Ukraine: Zelensky ya sha alwashin galaba kan Rasha
February 24, 2024Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi hasashen samun nasara a yakin da kasarsa ke gwambzawa da Rasha duk da cewa dakarun kasarsa na yaki cikin karancin kayan yaki daga yammacin duniya da kuma farmakin da Rashan ke kaiwa.
''Za mu yi nasara'', a cewar shugaba Zelensky, a yayin da yake jawabi a wannan rana ta asabar a filin jiragen sama na Kyiv da ya kasance tungar yakin tun kaddamar da farmakin Rasha a 24 ga watan Fabrairun 2022.
Karin bayani: Ukraine na neman karin tallafin daga kawayenta
Jawabin na shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da kai farmaki na musamman ta kasa domin murkushe duk wata barazana da ka iya tasowa daga Ukraine.
Karin bayani: Dakarun tsaron Rasha sun yi ruwan bama-bamai a Ukraine a matsayin martani
Shugaban rundunar tsaron Ukraine Oleksandr Syrsky, ya ce yana da yakinin cewa za su yi nasara, kasancewar bayan wuya sai dadi.